Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya yi kira ga magoya bayansa da su guji duk wata fitina ko tsokana da za ta iya tilasta musu mayar da martani ga masu kai hare-hare ko suka a fagen siyasa a Jihar Zamfara.
Matawalle ya kuma shawarci matasa da su kasance masu bin doka da oda tare da nuna kyawawan halaye, yana mai jaddada cewa ba zai amince da duk wani nau’i na rashin da’a ko tayar da tarzoma ba.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki daga Karamar Hukumar Birnin Magaji da wasu sassan Jihar Zamfara a gidansa da ke Karamar Hukumar Maradun.
Taron, wanda aka gudanar a matsayin gaisuwar Sallah, wata al’ada ce da Matawalle ya saba yi tsawon shekaru da dama.
Hakan ya ba shi damar tattaunawa da magoya bayansa kan makomar jam’iyyar APC da kuma ci gaban Jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
Tsohon gwamnan na Zamfara ya bukaci magoya bayansa da su kasance jakadu nagari na jam’iyyar a duk inda suke tare da mutunta ra’ayoyin da suka saba da nasu.
Ya kuma bukace su da su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga jam’iyyar APC tare da mara wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, baya.
A cewarsa, ci gaban jam’iyyar APC a Zamfara ba zai samu ba sai an samu hadin kai da fahimtar juna tsakanin ‘ya’yanta.
“Na gode muku baki daya da kuka zo yi min gaisuwar Sallah. Hakika na yaba da wannan ziyara, domin ta nuna cewa muna tare kuma muna aiki tare.
“Ina rokonku da ku ci gaba da wannan hadin kai,” in ji shi.
Matawalle ya kuma yi kira ga matasa da sauran magoya bayansa da kada su mayar da martani ga zage-zage da ake yi a kafafen sada zumunta.
“Mu mutane ne masu zaman lafiya, kuma an san mu da mutunta mutuncin dan Adam. Don haka, kada ku yi amfani da kafafen sada zumunta wajen kai hari ko zagin kowa, ko da kuwa wadanda suke zaginmu ne,” ya kara da cewa.
Ya jaddada cewa ya kamata ‘ya’yan APC su hada kai wajen karfafa jam’iyyar domin samun nasara a zabukan shekarar 2027.
A karshe, Ministan ya sake kira ga magoya bayan APC da su mara wa Shugaba Tinubu da Gwamna Dauda Lawal baya domin samun nasarar tazarce a zabukan 2027.

