Daga Usman Usman Garba
Yadda aikin gina Kotun Ɗaukaka Ƙara (Court of Appeal) da ke harabar Sakatariyar Audu Bako a Kano ke gudana.

Ana gudanar da aikin ne ta hanyar ƙoƙarin Hon. Abubakar Kabir Abubakar (Abba Bichi), ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Tarayya ta Bichi.

Ana sa ran kammala wannan aiki zai ƙara ƙarfafa tsarin shari’a tare da sauƙaƙa samun ayyukan Kotun Ɗaukaka Ƙara ga al’ummar Kano da ma jihohin da ke makwabtaka.


