Daga Umar Danladi Ado, Sokoto
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya tare da goyon bayan Rundunar Sojin Sama sun yi nasarar ceto Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, wadda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita tare da mijinta makonni kaɗan da suka gabata.
Ceton nata ya biyo bayan tsauraran matakan bincike da ceto da dakarun Operation FASAN YAMMA suka gudanar domin gano inda masu garkuwar suka boye ta.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ya bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare da matsin lambar da sojoji suka yi wa ‘yan bindigar ya tilasta musu ja da baya.
Sanarwar ta ce dakarun sun yi artabu da ‘yan bindigar a ƙauyen Tunga, lamarin da ya kai ga samun nasarar ceto Hajiya Amina Abubakar.
Sai dai, a yayin artabun, ‘yan bindigar sun harbi Hajiya Amina kafin su tsere tare da watsar da ita sakamakon matsin lambar da dakarun soji suka yi musu.
Nan take aka garzaya da ita zuwa asibitin sojoji domin kula da lafiyarta, inda ake ci gaba da yi mata magani kuma take nuna alamun samun sauƙi.
Shugabannin Rundunar Sojojin Najeriya sun jaddada aniyarsu ta tabbatar da cikakken murmurewar ta, tare da bayar da dukkan tallafin da ya dace ga iyalanta a wannan lokaci mai cike da ƙalubale.
Har ila yau, rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan farautar masu hannu a wannan ta’asa domin cafke su ko kuma hallaka su, tare da ƙara ƙaimi wajen kawar da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka daga al’ummomin da abin ya shafa, ba a jihar Katsina kaɗai ba har ma a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

