Daga Mahmud Gambo Sani

‎Fiye da yara dubu 112 ‘yan ƙasa da shekaru biyar ne, suka amfana da allurar rigakafin cutar shan-inna a Ƙaramar Hukumar Bichi.

‎Kamar yadda Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta rawaito, Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya, Malam Zakari Sani ne ya bayyana hakan a yayin taron tattauna yadda aikin rigakafin ya kansance a ƙaramar hukumar.

‎Zakari Sani, ya kuma tabbatar da gagarumar nasarar da yankin ya samu dangane da wasu ma’aunai da jiha ke auna ƙoƙarin kowace ƙaramar hukuma wajen gudanar da aikin rigakafin, wanda Ƙaramar Hukumar Bichi ta rabauta da ziyarar Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya na Kano, bisa tirenin da suke bai wa ma’aikata a kowace safiyar ranakun aikin na dukkan mazaɓun yankin 11.

‎Ya yi kira ga gwamnatin jiha ta kawo musu ɗauki na warware dambarwar rashin gidan sauro (net) da ake rabawa a wasu sassan yankin.

‎Ya kuma buƙaci ƙaramar hukumar ta saya musu janareto a matsayin ko ta kwana, ta yadda ko da solarsu ta samu matsala. A rigakafin da za a yi na gaba ya bukaci a horar da sabbin ma’aikatan da za’a dauka aikin da wuri domin cim ma nasara.

‎Sakataren Mulki na yankin, Alhaji Anas Muhammad Abdullahi da ya yi magana a madadin Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Mai Fata, ya bayyana farin ciki da jin daɗin nasarorin da aka samu. Kazalika ya shaida ƙaramar hukumar a tsaye take tsayin daka wajen tabbatar da nasarar aikin.

‎”Alhamdu lillahi, kuma muna fata a karo na gaba a sake samun nasara fiye da wadda aka samu yanzu. Batun janareto kuma in sha Allahu za a yi ƙoƙarin samar da shi, maganar net ma za mu yi ƙoƙari shi ma a matakin ƙaramar hukuma mu ga yadda za mu samar da shi domin kawar da matsalar.

‎Haka maganar sunayen waɗanda za su gudanar da aikin rigakafi na gaba, in sha Allahu za mu ga yadda yakamata a samu sunayen da wuri, a sanar domin yi musu bita da horo a kan lokaci, sannan ƙaramar hukuma za ta linka ƙoƙarin bayar da alewar da ake rabawa ga yara waɗanda ake yi wa allurar rigakafin yadda yakamata, domin ƙara samun nasarar aikin.” – Alhaji Anas Muhammad Abdullahi.

‎A ɓangaren Kansilan Lafiya, Malam Bashir Shu’aibu, ya gode wa Allah tare da tawagar gudanar da aikin rigakafin bisa nasarar da aka samu, bisa haka ya ƙara ƙarfafa musu gwiwar jajircewa da aiki tuƙuru yadda suka saba a kowane lokaci. Kana ya shawarci duk abin da yakamata a ba da gudunmawa a matakin ƙaramar hukuma da a bayar ɗari bisa ɗari.

‎A jawabin, Jami’in Kula da Harkar Sadarwa da Walwala na Shashen Lafiya dake Bichi, Malam Garba Ibrahim Ƙiru, ya bayyana gamsuwarsu dangane da yadda suka samu nasarar aikin kaso casa’in cikin ɗari, inda ya jaddada hakan na zuwa ne sakamakon gagarumar gudunmawar Majalisar ƙaramar hukumar tare da Fadar Hakimin Bichi, Galadiman Kano. Don haka ya yi matuƙar godiya a gare su tare da dukkan ma’aikatan da suke gudanar da aikin rigakafin.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version