Daga Mahmud Gambo Sani
Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta ɗauki nauyin kashe dala ɗaya kimanin naira dubu ɗaya da dari biyar ga ƙananan yara da ke faɗin jihar, domin inganta lafiya da kuzarinsu, ta hanyar haɗin gwiwa da Ƙungiyar (ICSA) mai taken Haɗaɗɗan Shirin Tallafa Wa Lafiyar Ƙananan Yara.
A sanawar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta Ƙaramar Hukumar Bichi Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, a yayin da ƙungiyar ta kai ziyara ƙaramar hukumar, da yake gudanar da jawabi, wakilin Kungiyar Lafiya ta Duniya na karamar hukumar, Malam Zakari Haruna, ya bayyana kwamitocin da aka kafa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar ne za su riƙa bibiyar shirin tun daga ɓangaren Lafiya a Matakin farko da suka haɗar da; ragakafin yau da kullum, makon lafiya na mata masu juna-biyu, yaƙi da zazzaɓin cizon sauro da kuma fannin cimaka domin kula da bai wa yara ingantaccen abinci, wanda zai ƙara musu lafiya da kuma kuzarinsu.
Ya kuma ce, yana daga manufar shirin, kula da inganta ayyukan asibitocin gwamnati da masu zaman kansu, ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki, da kiyaye zuwa aiki kodayaushe kuma a kan lokaci, tare da kyautatawa a cikin aikin da biya wa jama’a haƙƙoƙinsu, musamman ƙananan yara masu larurar rashin abinci mai gina jiki.
Don haka ya jaddada cewa, masu riƙe da madafun iko tare da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma ne ke da alhakin bibiyar wannan batu ɗari bisa ɗari, ta hanyar tattaunawa da mutane domin jin ra’ayoyinsu da za a riƙa tura wa gwamnati a matakin jiha, domin gudanar da wannan aikin yadda yakamata.
”Kowa dai ya san in ba abinci jiki ba zai yi aiki ba, kuma ba kowane irin abinci ake nufi a turmutsa wa yaro ba, face ingantacce mai gina jiki. Yana ɗaya daga cikin abin da kwamiti da masu madafun iko za su sa ido sosai akai, idan an samu tangarɗa su sanar da PHCC, ta yadda za a kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya'” – Malam Zakari Haruna.
Sakataren Mulki na yankin, Alhaji Anas Muhammad Abdullahi, da ya yi magana a madadin Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya bayyana sun yi na’am bisa gamsuwa da wannan shiri duba da irin yadda Shugaban yankin yake ƙoƙari wajen bunƙasa al’amuran jama’a, musamman ɓangaren lafiya da ilimi, wanda Gwabnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yake ta ƙoƙarin ya ga waɗannan abubuwan biyu (2) su ne manya-manyan ayyukan da yake so ya gabatar tare da mai da hankali a kai.
”Ƙaramar Hukumar Bichi ma ba a bar ta a baya ba; mai girma zaɓaɓɓen Ciyaman Alhaji Hamza Sule Mai Fata, yana matuƙar ƙoƙarin ganin an inganta cibiyoyinmu na lafiya, ƙanana da manyansu da kuma ilimi. Alhamdu lillahi wannan al’amari ya yi mana daɗi, kuma in sha Allahu za mu ba da goyon baya ɗari bisa ɗari domin ganin wannan shiri da aka zo da shi an samu nasara.”- Alhaji Anas Muhammad Abdullahi.
A nasa ɓangaren, Shugaban Sashen Lafiya a Matakin Farko, Malam Kabir Abubakar Gwarzo, ya nuna jin daɗinsa tare matuƙar godiya ga gwamnati, bisa farfaɗo da wannan ƙungiya mai alfanu a cikin al’umma. Ya kuma ba da tabbacin ba da gudunmawarsu matuƙa domin bunƙasa ƙoshin lafiyar yaran yankin.
Taron dai ya samu halarcin; mai Kula da Shirin, daga Ƙungiyar ICSA Fatima Aliyu Ladan, PHCC, STF, LIO, HE, DSS, Ci-Gari Foundation, Youth Leader Bichi, Sakataren Hakimin Bichi, Galaiman Kano da sauran masu ruwa da tsaki.
Trending
- KNSG denies abandoning Murtala Muhammed Library, faults contractor
- ACF suspends BoT chairman over alleged N1.4bn fund diversion
- Nigerian Army kills terrorist, recovers weapons in Kogi
- Appointing Garo as deputy is wisdom for Kano — Danbatta
- Kano strength bilateral ties with UK
- Katsina inaugurates committee for proposed light rail project
- Normalcy returns to Ugep, Idomi after communal clash
- 2027: Debate rages in Sokoto over ADC governorship ticket
