Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau

Hukumar makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara ta ayyana hutun makwanni biyu bayan wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai bakwai a wani masaukin dalibai da ke wajen harabar makarantar.

Shugaban makarantar, Dr. Aminu Yusuf, ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce lamarin ya faru ne a wani masaukin dalibai mai zaman kansa da aka fi sani da Chat House, wanda ke wajen harabar makarantar, ba a cikin harabar makarantar ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun kai hari ne a masaukin Chat House inda suka yi awon gaba da dalibai bakwai, yayin da dalibi guda ya samu nasarar tserewa daga hannunsu.

Dr. Aminu Yusuf ya karyata ikirarin cewa an kai harin ne cikin harabar makarantar, yana mai jaddada cewa lamarin ya faru ne a wajen makarantar.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar makarantar ta sanar da National Board for Technical Education (NBTE) da sauran hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakan da suka dace.

Dangane da harin, jami’an makarantar sun gudanar da taron gaggawa da masu ruwa da tsaki da shugabannin tsaro a yankin domin duba hanyoyin ceto daliban da aka sace da kuma karfafa matakan tsaro a makarantar da kewaye.

“Mahukuntan makarantar suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaron dalibai.

“Muna ci gaba da tuntubar jami’an tsaro, kuma muna da yakinin cewa nan ba da jimawa ba za a kubutar da daliban da aka sace,” in ji shugaban makarantar.

Ya kuma yi kira ga dukkan daliban da ke zaune a gidajen haya da ke wajen harabar makarantar da su koma babban dakin kwanan dalibai domin samun ingantacciyar kariya.

A cewarsa, makarantar ba za ta iya bayar da cikakken tabbacin tsaro ga daliban da ke zaune a gidaje masu zaman kansu da ke wajen harabar makarantar ba.

Haka kuma, ya bukaci al’ummar yankin da su kwantar da hankula tare da kasancewa masu lura da duk wani motsi da ake zargi, yana mai kira gare su da su rika sanar da hukumomin tsaro cikin gaggawa domin daukar matakin da ya dace.

“Haɗin kan al’umma da goyon bayan jama’a na da matuƙar muhimmanci a irin wannan lokaci,” in ji shi.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version