Daga Sanata Iroegbu
A watanni da suka gabata, an gabatar da wani ra’ayi da ya saba da abin da mutane da dama suka saba tunani. An yi hasashen cewa mafi ingantacciyar hanyar da Najeriya za ta bi wajen yaƙar yaɗa labaran ƙarya, labaran bogi da karkatar da bayanai ba lallai ba ne ta fito daga ma’aikatun gwamnati ko kamfanonin fasaha ba.
Maimakon haka, ana kyautata zatan cewar mafita na iya kasancewa a cikin masallatai, coci-coci da kuma bangarorin sarakunan gargajiya.
Wannan shi ne aka kira da Kano Model a harshen turanci, wanda ke kokarin ɗora shugabannin addini da na gargajiya a sahun gaba wajen gina juriyar al’umma da kare su daga yaɗa ƙarya da gurɓatattun bayanai.
A yau, wannan ra’ayi ya samu babban ci gaba. A Abuja, tsakanin ranar 24 zuwa 25 ga Yunin 2026, dandalin tantance gaskiyar bayanai na harshen Hausa mai suna Alkalanci ya gudanar da mafi girman horonsa kan tantance gaskiyar labarai da wayar da kan jama’a game da amfani da kafafen yaɗa labarai.
Tare da tallafin MacArthur Foundation da haɗin gwiwar Centre for Democracy and Development (CDD), taron ya haɗa malamai da limaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya a wuri guda karo na farko.
Wannan ya biyo bayan irin waɗannan horo da aka gudanar a Kano, Sokoto, Gombe, Kaduna da Maradi a Jamhuriyar Nijar. Zuwa yanzu, malamai da masu koyarwa sama da 120 sun amfana da shirin a birane shida da ƙasashe biyu. Abin da ya fara a matsayin ƙaramin gwaji a masarauta guda yanzu ya zama wani gagarumin yunƙuri.
Lokacin gudanar da wannan shiri ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, lokacin da yaɗa ƙarya da jita-jita ke ƙaruwa.
A yankin Sahel kuma, gwamnatocin soji na fama da ta’addanci yayin da ƙasashen duniya ke fafatawa wajen samun tasiri ta hanyar yaƙin bayanai kamar yadda suke yi ta diflomasiyya ko makamai.
Haka kuma, fasahar Artificial Intelligence (AI) ta bai wa masu son tayar da zaune tsaye damar ƙirƙirar bidiyoyi, hotuna da sautin murya na bogi cikin sauƙi. Saboda haka, wannan ba matsalar kafafen yaɗa labarai kaɗai ba ce, illa babbar barazana ce ga tsaron ƙasa.
Muhimmancin taron Abuja ba ya tsaya ga yawan mahalarta kaɗai, har ma da irin goyon bayan manyan cibiyoyin addinin Musulunci na Najeriya.
Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi da kuma Jama’atu Nasril Islam (JNI) sun buƙaci malamai su zama masu kare gaskiya.
Ta bakin Sakatare Janarinta, Farfesa Is-haq Oloyede, NSCIA ta tuna cewa Suratul Hujurat ta umurci muminai su tabbatar da sahihancin labari kafin su yanke hukunci ko ɗaukar mataki. Don haka, tantance gaskiya ba sabon abu ba ne, umarni ne daga Allah.
Wannan fahimta ta addini ta sauya yadda ake kallon yaƙi da yaɗa ƙarya. Shekaru da dama gwamnatoci sun yi ƙoƙarin magance matsalar ta hanyar dokoki, takunkumi da fasaha. Duk da muhimmancinsu, babu ɗaya daga cikinsu da zai iya maye gurbin abin da ake kira amincewar jama’a.
Yawancin mutane ba koyaushe suke yarda da gwamnati ba, amma suna yarda da maganar malamai da sarakuna. A Arewacin Najeriya da sauran sassan Afirka, babu waɗanda jama’a suka fi amincewa da su kamar malamai da sarakunan gargajiya.
Kowace Juma’a, kowace Lahadi da sauran lokutan taruka, miliyoyin mutane na sauraron limamai, fastoci, malamai da sarakuna.
Idan waɗannan shugabanni suka buƙaci mutane su tsaya su bincika kafin su tura wani saƙo ko su gaskata wani bidiyo ko jita-jita, suna gina wata katangar kariya da babu wata na’ura ko fasaha da za ta iya maye gurbinta.
A nan ne rawar da cibiyoyin gargajiya ke fitowa fili. Shirin ya samu goyon bayan masarautu daban-daban. Sarkin Kano ya wakilta a taron farko, Sarkin Musulmi a wani taro, haka kuma Masarautar Gombe.
Lokacin da Sarkin Alkali ko wakilin sarki ya yi magana ga malamai, maganarsa na da tasirin da umarnin gwamnati ba zai iya kaiwa ba. Kamar yadda wakilin Sarkin Gombe ya bayyana, faɗin gaskiya ba kawai ɗabi’a ba ce, ibada ce.
A halin yanzu kuma, barazanar na ƙara sauyawa. Editan Alkalanci, Alhassan Bala, ya yi gargadin cewa zaɓen 2027 zai zo da ƙarin yaɗa ƙarya daga cikin gida da kuma katsalandan daga ƙasashen waje.
Fasahar Deepfake, wato ƙirƙirar sauti, bidiyo da jawabai na bogi, ta zama mai sauƙin amfani, lamarin da ke ƙara haɗari.
Sakatare Janar na JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya buƙaci malamai su guji nuna son kai a siyasa, su tabbatar da gaskiya kafin su yi magana, sannan ya gargadi ‘yan siyasa da kada su jefa shugabannin addini cikin rikicin siyasa.
A ƙasa irin Najeriya, inda bidiyo guda na bogi zai iya haddasa tashin hankali cikin dare ɗaya, samun malamai da aka horar wajen tantance gaskiya wata babbar kadara ce ga tsaron ƙasa.
Abin da ke faruwa a yankin Sahel ya ƙara nuna muhimmancin wannan mataki. A Mali, Burkina Faso da Nijar, yaɗa ƙarya ya zama makamin yaƙi da ake amfani da shi wajen halatta juyin mulki, raunana dimokuraɗiyya da kuma haddasa gaba tsakanin al’umma. Yawancin irin waɗannan yaɗa bayanai na samun goyon bayan wasu ƙasashen waje masu neman tasiri a Afirka.
Saboda haka, kai wannan horo zuwa Maradi a Nijar ba ƙaramin ci gaba ba ne.
Wannan yana kai Tsarin Kano zuwa yankin da yaƙin bayanai ya fi ƙarfi, ta hanyar amfani da abin da masu yaɗa farfaganda ba za su iya mallaka ba—murya mai aminci da ke magana da harshen gida.
Haka kuma, wannan shiri ya nuna irin rawar da ƙungiyoyin farar hula za su iya takawa. Ba aikin gwamnati ba ne, illa yunƙurin wata ƙungiya ta cikin gida da ke ƙarfafa juriyar al’umma ta hanyar bai wa shugabannin da jama’a suka amince da su damar zama masu koyarwa, masu tabbatar da gaskiya da masu kare al’umma daga ƙarya. Duk irin wannan ƙoƙari, a zahiri, saka jari ne wajen tabbatar da zaman lafiya.
Darasin da Kano, Abuja, suka koyar yana da matukar muhimmanci. Yaƙi da yaɗa ƙarya ba gwamnati kaɗai za ta iya cin nasararsa ba, kuma ba za a iya ɗora shi gaba ɗaya a kan ‘yan jarida, masu tantance gaskiya ko kamfanonin fasaha ba. Dole ne ya zama alhakin kowa, ya haɗa shugabannin addinin Kirista, mata, matasa da sarakunan gargajiya a faɗin Najeriya.
A wannan lokaci da ƙarya ke bazuwa fiye da gaskiya cikin sauri, babbar damar da Afirka ke da ita ba sabbin fasahohi kaɗai ba ne, amma cibiyoyinta na addini da al’adun gargajiya da suka daɗe suna da amincewar jama’a.
Masu kare gaskiya kullum na ƙaruwa. Abin da ya rage wa Najeriya, yankin Sahel da ma Afirka baki ɗaya shi ne tabbatar da cewa wannan runduna ta ci gaba da ƙaruwa.
Sanata Iroegbu masani ne kan harkokin tsaro, siyasar ƙasa da ƙasa da ci gaba, ya yi wannan rubutun ne daga Abuja.

