Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Gabanin zaben 2027, dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Zamfara, Barista Mahadi Aliyu Mohammed, ya karyata rahotannin janyewarsa daga takara, yana mai cewa har yanzu yana nan a matsayin sa na Halittaccen dan takara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun dan takarar gwamnan jihar ADC, Salisu Mohamed Mada ya fitar a daren ranar Laraba a Gusau, ya bayyana cewa Barista Mahadi Aliyu ya ci gaba da zama zababben dan takarar jam’iyyar ADC a zaben gwamna na 2027 a jihar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An jawo hankalin mai girma Gwamna, Barr. Mahdi Aliyu Muhammad, wanda ya zama zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Zamfara, a kan wani rahoto na batanci, kage, da yaudara a halin yanzu da ake yawo a kafafen sada zumunta daban-daban na cewa ya janye takararsa na tsayawa takarar gwamna a zaben 2027.
“Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa wannan rahoton karya ne, maras tushe, barna, kuma aikin wasu ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau wadanda kawai manufarsu ita ce su bata jama’a, su haifar da rudani a cikin harkokin siyasa, da kuma kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya.
“Don kaucewa shakku, Barr. Mahdi Aliyu Muhammad ya halarci zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar ADC, ya yi nasara, aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a hukumance, sannan kuma ya amince da wa’adin da ‘yan jam’iyyar suka ba shi, “Har yanzu shi ne sahihin dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Zamfara.
An Kuma bukaci wadanda keda iron wannan mugun kazafi DA sharri na babu gaira babu dalili dasu ji tsoron Allah su daina domin irin wannan Yana kawo illa ga dimokuradiya Kuma ya sabawa doka.

