Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil’adama ta kasa (SAT) ta yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) domin yaki da cutar tarin fuka (TB), cin zarafin mata da jinsi (GBV), da kuma take hakkin dan Adam a fadin Jihar Zamfara.
An yi wannan kira ne yayin wata ziyarar ban girma da kungiyar ta kai ofishin NHRC da ke Gusau, babban birnin jihar.
Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Kodinetan Shirin Yaki da Cutar Tarin Fuka na Jihar Zamfara, Abdullahi Lawali Bungudu, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa da hukumar tare da neman goyon baya wajen aiwatar da tsarin Community-Led Monitoring (CLM) domin inganta ayyukan kula da lafiyar al’umma.
Ya ce ana sa ran wannan hadin gwiwa zai kara wayar da kan masu ruwa da tsaki game da manufofi, muhimmanci da kuma fa’idodin shirin a jihar.
A nasa jawabin, Jami’in Tsare-tsare na Jiha (SPO), Yahaya Muhammad, ya yi wa Kodinetan NHRC na jihar, Abdullahi Abubakar, karin haske kan sakamakon ayyukan wayar da kai da kungiyoyin al’umma (CBOs) suka gudanar kan batutuwan cin zarafin mata da jinsi da kuma kare hakkin dan Adam.
Muhammad ya bayyana cewa ayyukan wayar da kan jama’ar sun gano muhimman kalubalen da suka shafi hakkin bil’adama a tsakanin al’ummomi, inda ya bukaci NHRC da ta dauki matakan da suka dace domin magance matsalolin da aka gano.
Ya jaddada cewa kare hakkin masu fama da cutar tarin fuka, tabbatar da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya da magunguna, da kuma kawar da kyama da nuna wariya ga masu dauke da cutar na da matukar muhimmanci wajen rage tasirin tarin fuka a jihar.
Jami’in ya kara da cewa kungiyar masu fama da cutar tarin fuka ta Zamfara memba ce ta hadakar kungiyoyin farar hula masu yaki da cutar tarin fuka a Najeriya, wadda ke hada kungiyoyi masu zaman kansu da na farar hula da suka dukufa wajen ganin an kawar da cutar a kasar.
Muhammad ya yabawa NHRC kan yadda take gudanar da ayyukanta, tare da tabbatar da cewa kungiyar za ta ci gaba da bai wa mambobinta da sauran abokan hulda horo da kayan aiki da suka dace domin magance kalubalen da ake fuskanta.
“Wannan ziyara ba wai don karfafa alaka kawai aka yi ta ba, har ma domin shimfida harsashin dorewar hadin gwiwa wajen magance matsalolin kiwon lafiyar jama’a da kuma kare hakkin bil’adama a Jihar Zamfara,” in ji shi.
A nasa martanin, Kodinetan NHRC na Jihar Zamfara, Abdullahi Abubakar, ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon bayan hukumar ga shirin, tare da yabawa kungiyar bisa kokarinta wajen wayar da kan jama’a da kare hakkin masu fama da cutar tarin fuka.
Ya kuma bukaci mambobin kungiyar sa ido na al’umma (CLMT) da su ci gaba da tuntubar hukumar a duk lokacin da suke bukatar tallafi ko hadin gwiwa yayin gudanar da ayyukansu.
Har ila yau, Abubakar ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a gidan gyaran hali na Gusau bayan wata ziyara da ya kai kwanan nan, inda ya lura da karancin kayan koyon sana’o’i da damar ilimantarwa idan aka kwatanta da wasu cibiyoyin gyaran hali da ke wasu jihohin kasar nan.
Taron ya kare ne da bangarorin biyu sun sake jaddada kudirinsu na ci gaba da hada kai domin inganta kare hakkin dan Adam, kyautata lafiyar al’umma, da kuma kara kaimi wajen yaki da cutar tarin fuka da cin zarafin mata a Jihar Zamfara.

