Daga Ahmad Muhammad Sani Gwarzo, ANIPR
Turakin Gwarzo, Ambassador Alarammah Dahiru Rabi’u Gwarzo, ya yi kira ga al’umma da su guji ɗabi’ar hassada tare da rungumar ƙauna, haƙuri da son alheri ga juna domin samun zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Ya bayyana hakan ne a yayin wani zaman majalisi da aka gudanar a ƙofar gidan Alhaji Adamu Lawan Gwarzo, inda malamai, dattawa, matasa da sauran jama’a suka halarta domin sauraron nasihohi da shawarwari kan al’amuran rayuwa da addini.
A cewarsa, hassada na daga cikin manyan cututtukan zuciya da ke haddasa rarrabuwar kai, gaba da rashin zaman lafiya a cikin al’umma. Ya jaddada cewa addinin Musulunci ya yi gargaɗi mai tsanani game da wannan mummunar ɗabi’a.
Turakin Gwarzo ya bayyana cewa hassada tana raunana imanin mutum, domin mai hassada ba ya gamsuwa da ƙaddarar Allah da yadda Ya raba ni’imominsa ga bayinsa.
Haka kuma, tana hana mutum samun nutsuwar zuciya, kasancewar mai wannan ɗabi’a kullum yana cikin damuwa da baƙin ciki saboda alherin da wasu suka samu.
Ya ƙara da cewa hassada tana haifar da ƙiyayya da gaba a tsakanin jama’a, tare da lalata zumunci tsakanin ‘yan uwa, abokai da maƙwabta.
Har ila yau, tana iya jawo mutum zuwa aikata zunubai kamar gulma, ƙage, cin mutunci da ƙulla makirci domin cutar da wasu.
A cewarsa, hassada tana hana mutum godiya ga ni’imomin da Allah Ya yi masa, saboda yawan kallon abin da wasu suke da shi maimakon abin da Allah Ya hore masa.
Ya kuma bayyana cewa wani lokaci tana sa mutum ya ƙi gaskiya ko ya ƙi amincewa da nagartar wani saboda son zuciya da kishin banza.
Turakin Gwarzo ya yi nuni da cewa damuwa da baƙin cikin da hassada ke haifarwa na iya yin illa ga lafiyar jiki da ta tunani, tare da hana mutum mayar da hankali wajen bunƙasa rayuwarsa.
Ya gargadi al’umma cewa idan ba a tuba daga hassada ba, tana iya zama sanadin asarar alherin duniya da lahira.
Dangane da hanyoyin magance hassada, ya shawarci al’umma da su yawaita ambaton Allah da yin zikiri, su yarda da ƙaddarar Ubangiji, su riƙa yi wa juna addu’ar alheri, tare da yawan gode wa Allah bisa ni’imominsa.
Ya kuma bukaci jama’a da su riƙa son alheri ga ‘yan uwansu Musulmi kamar yadda suke so wa kansu, yana mai cewa wannan na daga cikin siffofin cikakken imani.
Turakin Gwarzo ya tunatar da mahalarta majalisar hadisin Manzon Allah (SAW) da ke cewa: “Ku guji hassada, domin hassada tana cinye ayyukan alheri kamar yadda wuta take cinye itace.”
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya tsarkake zukatan al’umma daga hassada, ƙiyayya da son zuciya, Ya haɗa kan jama’a cikin ƙauna da fahimtar juna, tare da tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma.
Allah Ya kiyaye mu daga hassada, Ya ƙawata zukatanmu da imani, haƙuri da son alheri ga juna. Amin.

