Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da shugaban makarantar kimiyya da fasaha ta Abdu Gusau Polytechnic da ke Talata Mafara, Dakta Sirajo Abdullahi Shinkafi, bisa zargin rashin da’a da kuma rashin biyayya ga gwamnati.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar M. Nakwada, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa dakatarwar ta fara aiki nan take.
Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta amince da dakatar da Dakta Sirajo Abdullahi Shinkafi daga mukaminsa na shugaban kwalejin bisa laifukan da ake zarginsa da aikatawa na rashin da’a da rashin biyayya.
Malam Nakwada ya kuma tabbatar wa jama’a cewa gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin karatu da sauran ayyukan gudanarwa na makarantar ba tare da wata tangarda ba.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da cewa ayyukan cibiyar suna tafiya yadda ya kamata duk da dakatarwar da aka yi wa shugaban makarantar.

