Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan-Disu, ya halarci jana’izar jami’an ‘yan sanda uku da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kan hanyar Anka zuwa Bagega yayin da jami’an ke gudanar da aikin gano da kuma tarwatsa wasu bama-bamai da ake zargin ‘yan bindiga sun dasa a yankin.
An gudanar da sallar jana’izar a ranar Talata a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke Gusau, karkashin jagorancin CSP Suleiman Alhassan Haruna.
Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Nakwada, ya wakilta.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Ahmed Mohammed Bello, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar jami’an, yana mai cewa rashin nasu babban gibi ne ga rundunar da kuma al’ummar da suke karewa.
Ya bayyana sunayen jami’an da suka rasu kamar haka: SP Abdulrazak Musa Hassan, OC EOD Insfekta Auwal Ahmad da kuma Insfekta Murtala Musa.
A cewarsa, jami’an sun bayar da sadaukarwa mafi girma wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Rundunar ‘yan sandan Zamfara za ta ci gaba da tunawa da irin hidimar da suka yi da kuma sadaukarwar da suka yi wa kasa.
“Jarumai sun fadi, amma abin da suka gada zai ci gaba da rayuwa.”
Ya kara da cewa ba za a taba mantawa da jarumtaka, sadaukarwa da jajircewar jami’an wajen wanzar da zaman lafiya da kare rayukan jama’a ba.
A nasa bangaren, Gwamna Dauda Lawal, ta bakin wakilinsa, ya bayyana rasuwar jami’an a matsayin babban rashi ga kasa, yana mai cewa hakan wata shaida ce ta kishin kasa da sadaukar da kai da suka nuna wajen gudanar da aikinsu.
Ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, abokan aikinsu da daukacin rundunar ‘yan sandan Najeriya, yana mai jaddada cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta tafi a banza ba, kuma za ta ci gaba da zama abin koyi ga masu zuwa a gaba.

