Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Wata kungiya da ke karkashin Arewa Core Vanguard for Good Governance ta gargadi masu yi wa Sanata Abdulaziz Yari Abubakar batanci da cin mutunci, tana mai cewa Sanatan na taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma tabbatar da nasarar manufofin Renewed Hope.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Laraba, Kodinetan kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Ibrahim Ahmadu, ya bayyana Yari a matsayin babban jigon siyasar Arewa ga Shugaba Tinubu.
Ya ce goyon bayan da Sanata Yari ke bai wa shugaban kasa ba wai kawai nuna amincewa ba ne, illa wata dabarar siyasa ce da ke hada kan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ci gaban kasa.
A cewarsa, ta hanyar Tinubu Renewed Hope Network (TRN), Sanata Yari ya jagoranci wani gagarumin yunkuri na siyasa da nufin hada kan magoya bayan shugaban kasa a fadin Najeriya, tare da yada nasarorin da gwamnatin ta samu zuwa kananan hukumomi 774 na kasar.
“Yari ya taka muhimmiyar rawa wajen yakin neman zaben Shugaba Tinubu a Arewa, musamman Arewa maso Yamma. Ya kuma shirya manyan tarukan addu’o’i da suka hada da malamai da sarakunan gargajiya domin neman taimakon Allah ga shugaban kasa wajen gudanar da mulkin kasar nan,” in ji Ahmadu.
Ya kara da cewa kungiyoyin da ke da alaka da Sanata Yari suna ci gaba da kare manufofin gwamnatin Tinubu tare da kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa gyare-gyaren tattalin arziki da na hukumomi baya.
Kungiyar ta kuma tunatar da jama’a cewa Sanata Yari ya sha musanta zarge-zargen da ke cewa yana daukar nauyin zanga-zangar adawa da gwamnati, yana mai jaddada cewa dangantakarsa da Shugaba Tinubu ta ginu ne kan mutunta juna da kuma kishin kasa.
Ta ce a wani taron addu’a da Arewa Think Tank ta shirya a ranar 30 ga Maris, 2026 domin bikin cikar Shugaba Tinubu shekaru 74, Yari ya bayyana cewa shugaban kasa ya gaji manyan kalubalen tsarin mulki da tattalin arziki, wanda ya sa dole yake daukar matakai masu tsauri domin gyara su.
Har ila yau, kungiyar ta ce Sanata Yari ya yaba da kokarin gwamnatin Tinubu wajen yaki da ta’addanci da matsalolin tsaro a Arewa maso Yamma, yana mai bayyana cewa shugaban kasa na aiki tukuru tare da karbar bayanai daga dukkan bangarori masu muhimmanci domin ciyar da Najeriya gaba.
A karshe, kungiyar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su ci gaba da marawa Sanata Abdulaziz Yari baya wajen karfafa goyon bayan siyasa ga gwamnatin tarayya da kuma tabbatar da dorewar manufofin ci gaban kasa.

