Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan manoma a gonakin da ke yankin Goron Namaye, a karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, inda suka kashe mutane 17 tare da jikkata wasu 13.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin da manoman ke gudanar da ayyukansu na noma a gonakin da ke wajen garin.
Da yake tabbatar da faruwar harin, Shugaban Karamar Hukumar Maradun, Hon. Sanusi Ahmed Dosara, ya bayyana alhininsa kan harin da ya yi sanadin asarar rayuka da jikkatar mutane.
Ya ce nan take bayan samun rahoton harin ya tuntubi hukumomin tsaro da ke yankin domin su dauki matakan gaggawa na dakile masu aikata laifin da kuma tabbatar da tsaron manoma yayin kakar noma ta bana.
“Da samun bayanan harin, na sanar da dukkan hukumomin tsaro domin su dauki matakan da suka dace wajen hana sake aukuwar irin wannan lamari da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji Dosara.
Wani mazaunin yankin, Alhaji Wada, ya ce ya dawo daga gonarsa da ke kusa da wurin da lamarin ya faru bayan ya kai ma’aikatansa gona domin gudanar da ayyukan noma.
A cewarsa, ya ji mutane suna ihu tare da gudu zuwa cikin gari kafin daga bisani ma’aikatansa su dawo suna sanar da shi cewa ‘yan bindiga dauke da makamai sun mamaye yankin tare da korar manoman da ke aiki.
Shi ma wani mazaunin garin, Dan Inna Gora, ya ce ya kirga gawarwaki akalla 17 a gonakin da ke da tazarar ‘yan kilomita daga garin, yayin da mutane 13 da suka samu raunukan harbin bindiga aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Ya kara da cewa mazauna yankin sun samu rahotannin cewa shugaban maharan ya aika da sakon gargadi ga al’ummar Goron Namaye, yana umurtarsu da su daina zuwa gonakinsu domin yin noma a daminar shekarar 2026.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara bai yi nasara ba, domin jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, bai amsa kiran waya da aka yi masa ba.

