Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu bakwai suka samu raunuka daban-daban sakamakon fashewar wani abin fashewa da wata motar daukar fasinjoji ta taka a hanyar Bagega zuwa Anka, a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Wani mazaunin kauyen Bagega, Sambo Dan Bagega, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na yammacin ranar Litinin, lokacin da motar kasuwa da ke jigilar fasinjoji daga Bagega zuwa Anka ta taka abin fashewar da ake zargin bam ne, lamarin da ya haddasa tashin hankali a yankin.
A cewar mazauna yankin, ana kyautata zaton cewa ‘yan bindiga ne suka dasa bam din, kasancewar suna ci gaba da kai hare-hare tare da addabar al’ummomin yankin.
“Fasinjojin suna kan hanyarsu daga Bagega zuwa Anka lokacin da abin fashewar ya tashi.
“Mutum daya ya mutu nan take, yayin da wasu bakwai suka samu raunuka daban-daban. A halin yanzu wadanda suka jikkata na karbar kulawa a cibiyar lafiya da ke Bagega,” in ji wata majiya daga yankin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce fashewar abin da ake zargin bam ne ta yi sanadin mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu bakwai.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro na hadin gwiwa sun dauki matakin gaggawa bayan samun rahoton lamarin, inda aka tura kwararrun jami’ai na musamman zuwa wurin tare da hadin gwiwar rundunar sojoji.
A cewarsa, an umurci jami’an tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru, tare da kawar da duk wata barazana da ka iya kasancewa a yankin domin tabbatar da tsaron lafiyar matafiya da mazauna garuruwan da ke kusa.
DSP Abubakar ya kara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da aiki domin dawo da zaman lafiya a hanyar Bagega zuwa Anka tare da hana sake afkuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.

