Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa tana ci gaba da ɗaukar matakan inganta harkokin kasuwanci da jawo zuba jari tare da tallafa wa ‘yan kasuwa domin bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Malam Mummuni (Masaramar Mudi), ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da Shirin Inganta Harkokin Kasuwanci na Jiha (SABER), wanda aka gudanar ranar Talata, 23 ga Yuni, 2026, a zauren Dakta Garba Nadama da ke Gusau.
Ya ce gwamnatin jihar ta fara aiwatar da gyare-gyare da sauye-sauye da nufin samar da sauƙin gudanar da kasuwanci da kuma jawo jarin kamfanoni masu zaman kansu zuwa jihar.
A cewarsa, shirin SABER ya ƙunshi muhimman fannoni da suka haɗa da kula da filaye, gyaran tsarin gudanarwa, saka hannun jari a kayayyakin more rayuwa na fiber optic, haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, bunƙasa zuba jari, inganta tsarin haraji da kuma kyautata yanayin gudanar da kasuwanci.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙarfafa cibiyoyi masu muhimmanci da suka haɗa da Hukumar Kula da Filaye da Bayanan Kadarori ta Zamfara (ZAGIS), Hukumar Tsara Birane da Yankuna, Hukumar Bunƙasa Zuba Jari, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Jiha, Kamfanin Samar da Ruwan Sha da kuma Sashen Duba Ababen Hawa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta yi amfani da albarkatun da aka samu ta hanyar shirin SABER mai tallafin Bankin Duniya wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi bunƙasa kasuwanci da ci gaban tattalin arziki a faɗin jihar.
Malam Mani ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa ‘yan kasuwa ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafawa da bayar da tallafi.
A cewarsa, an ba ƙananan ‘yan kasuwa 2,000 tallafin naira 150,000 kowannensu, yayin da wasu 1,000 suka samu naira 500,000 kowannensu. Haka kuma, manyan ‘yan kasuwa 60 sun karɓi tallafin naira miliyan biyar kowannensu.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma taimaka wajen samar da lasisin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje ga ‘yan kasuwa 20 domin faɗaɗa kasuwancinsu zuwa kasuwannin duniya.
Daga nan sai ya buƙaci duk waɗanda suka ci gajiyar tallafin gwamnati da su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata domin bunƙasa sana’o’insu, samar da ayyukan yi da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin Zamfara da Nijeriya baki ɗaya.
Mataimakin gwamnan ya yi maraba da tawagar gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron, inda ya buƙace su da su ci gaba da sa ido kan ayyukan da ake aiwatarwa domin auna tasirinsu ga al’umma.
Ya kuma sake jaddada kudurin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da zai bai wa masu zuba jari da ‘yan kasuwa damar bunƙasa tare da tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a jihar Zamfara.

