Daga Rabiu Sanusi
Daraktan Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano, Dr. Surajo Sulaiman, ya sake jaddada kudirin hukumar na kara zage damtse wajen wayar da kan al’umma, bunkasa hadin kan jama’a, da kuma tallafawa manyan shirye-shiryen ci gaban gwamnati a fadin jihar.
Da yake bayani kan ayyukan hukumar, Dr. Sulaiman ya bukaci al’ummar jihar da su hada kai wajen magance matsalolin da ke addabar yankunansu, yana mai cewa cigaba mai dorewa ba zai samu ba sai da hadin kai da jajircewar jama’a.
Ya shawarci al’umma da su rika kafa kwamitoci na gari domin isar da koke-kokensu, bukatunsu da shawarwarinsu ga hukumomin da suka dace, yana mai jaddada cewa tsari mai kyau wajen sadarwa na taka muhimmiyar rawa wajen samun saukin matsaloli da ci gaba.
A cewarsa, hukumar na amfani da hanyoyi daban-daban wajen wayar da kan jama’a kan muhimman batutuwa, musamman a fannoni na lafiya, tsaftar muhalli da walwalar al’umma.
Sai dai ya amince cewa hukumar na fuskantar wasu kalubale, musamman wajen kara wayar da kan jama’a domin su dauki nauyin kula da lafiyarsu da kuma tsaftace muhallansu.
Dr. Sulaiman ya kuma bayyana cewa a kokarin da gwamnati ke yi na yaki da cutar zazzabin cizon sauro tare da kare lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara, wani kwamiti karkashin hukumar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi na tattara bayanai domin dakile yaduwar cutar a fadin jihar.
Ya ce bayanan da za a tattara za su taimaka wa gwamnati wajen daukar matakan da suka dace, ciki har da rabon magunguna kyauta, gidajen sauro da kuma feshi da maganin sauro a sassa daban-daban na jihar.
Daraktan ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarin da yake yi wajen sauke nauyin ‘yan fansho a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar.
Haka zalika, ya jinjinawa gwamnan kan daukar nauyin karatun dalibai zuwa kasashen waje da kuma biyan kudin jarabawar WAEC da NECO ga daliban jihar.
A karshe, Dr. Sulaiman ya yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai, shawarwari masu anfani da kuma goyon baya domin samun zaman lafiya, cigaba da wadata a jihar.

