Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Dan takarar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Anka/Talata Mafara a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Abdulrahaman Yahaya, ya garzaya kotu domin kalubalantar matakin da ya ce an dauka ba tare da gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba.
Matakin na shari’a ya biyo bayan zargin da aka yi na kokarin amfani da wasu katunan zama mambobin jam’iyya da ake zargin an kirkire su ta hanyar da ba ta dace ba domin sauya sakamakon tsarin fitar da dan takara.
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na kwamitin yakin neman zaben Hon. Yahaya, Nura Rabi’u Cibiki, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa daukar matakin kotu ya zama dole domin kare hakkin mambobin jam’iyyar da kuma tabbatar da gaskiya a tsarin siyasa.
Sanarwar ta ce magoya bayan jam’iyyar ADC a kananan hukumomin Anka da Talata Mafara suna da masaniya kan sahihin karfin ‘yan takara, kuma sun kuduri aniyar kare martabar jam’iyyar.
A cewar sanarwar, Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau ta amince da karbar karar, inda ta sanya ranar 23 ga watan Yuni, 2026 domin fara sauraron shari’ar.
Hon. Abdulrahaman Yahaya ya bayyana cewa ba za su amince da duk wani yunkuri na magudi ko kirkirar takardun da za su iya bata tsarin dimokuradiyya ba, yana mai cewa hakan na iya kara haddasa rashin jituwa a cikin jam’iyya da mazabar Anka/Talata Mafara.
A nasa bangaren, wasu magoya bayan ADC sun bayyana cewa duk da cewa shari’a na iya daukar lokaci, amma gaskiya za ta bayyana a karshe.

